Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Déby Itno, ya kai ziyarar bazata a safiyar Talata 2 ga Satumban 2025, zuwa cibiyar kasuwanci ta CNPS da ke N’Djamena babban birnin kasar.
A yayin ziyarar shugaban ya nuna rashin jin daɗinsa kan jinkirin da ake samu wajen kammaluwar aikin cibiyar, da kuma wasu matsaloli na inganci da rashin bin ka’idoji daga dan kwangilar.
Shugaban ya kuma gargadi masu kwangila da cewa ba zai lamunci sakaci ko yin wasa da muhimman ayyukan raya kasa ba.



