Tsohon Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika, ya musanta zargin cewa shirin Nigeria Air da gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ta ƙaddamar ba damfara ba ce.
A wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Talata, Sirika ya ce gwamnati ta bi doka da ka’ida wajen aiwatar da aikin, tare da sa hannun hukumar ICRC.
Ya ce abin da ake faɗa na cewa an kashe Naira biliyan 100 a kan aikin ba gaskiya bane, jimillar kasafin kuɗin da aka ware biliyan 5 ne, kuma abin da aka fitar bai wuce biliyan 3 ba, inda ya bar sama da biliyan 1 a ma’aikata lokacin da ya bar ofis.
An ƙaddamar da Nigeria Air a ƙarshen mulkin Buhari, lamarin da ya jawo cece-kuce daga al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.
Bayan barin ofis a 2023, EFCC ta gurfanar da Sirika bisa tuhumar karkatar da kuɗaɗen kwangilar da kuma bai wa kamfanonin da ’ya’yansa da surukinsa ke da hannun jari a ciki.




Hmmmm Sirika ke nan, wannan Gurguwar Hujjar taka sai ka bari ranar da aka wayi gari, ka ganka a gaban Allah to sai ka fada masa cewar Kwangilar Nigerian Air babu Damfara a ciki, kaji ko?.