Ministan yada labaran Najeriya Mohammed Idris, ya musanta zargin cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu na amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa wajen musgunawa ‘yan adawa.
Wannan martanin nasa na zuwa ne bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin da amfani da hukumar EFCC wajen musgunawa ‘yan adawa a shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Idris ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba yayin buɗe taron tattaunawa da hukumar ICPC ta shirya a Abuja kan rawar da kwamishinonin yaɗa labarai na jihohi za su taka wajen yaƙi da rashawa.
Ya ce gwamnatin Tinubu ba ta tsoma baki domin tabbatar da cewa hukumomin EFCC da ICPC suna gudanar da ayyukansu ba tare da fuskantar matsin lamba daga gwamnati ba.



