Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce manufofin tattalin arziƙin gwamnatinsa sun fara haifar da sakamako mai kyau, inda tattalin arziƙin ƙasar ya fara daidaita tare da jawo mata kima a idon duniya.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya karɓi bakuncin Sarkin Ogbomosoland, Oba Ghandi Afolabi Oladunni Olaoye, tare da wasu sarakunan gargajiya a fadarsa da ke Abuja.
Ya ce cin hanci da rashawa sun lalata tattalin arziƙin ƙasar, amma yanzu saboda matakan da aka dauka kasar ta fara farfadowa.
Shugaban ya kuma bayyana kafa asusun NELFUND a matsayin matakin tabbatar da cewa babu wani ɗalibi zai daina karatu saboda talauci, yana mai cewa ilimi shi ne makami mafi dacewa wajen yakar talauci.




Gaskiya wannan Maganar ta Mr. T-Pain Ƙarya Tsagwaronta, saboda Talakawan Nigeria sun shiga Hali na Ƙuncin da basu taɓa shiga ba. Sakamakon Manufofin marasa amfani ga Talaka