Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa matsalar ayyukan ’yan bindiga da ke addabar jihar za ta zama tarihi muddin ya samu damar bayar da umarni kai tsaye ga jami’an tsaro.
A cewar gwamnan, yana da cikakkiyar masaniya kan duk inda manyan shugabannin ’yan bindiga suke a jihar, saboda gwamnati tana bibiyarsu a wurare daban-daban na jihar.
Ya ce duk da wannan, rashin ikon da yake da shi na umartar jami’an tsaro ya hana daukar matakin da ya dace a kansu, amma da zai samu wannan ikon cikin watanni biyu za a gama da su.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa ta dauki matakai masu yawa wajen tallafawa jami’an tsaro da kayan aiki, ciki har da raba motoci 150, daukar dubban jami’an sa kai na CPG, da kuma shigo da mafarauta fiye da 2,000 daga jihohin Borno da Yobe domin taimaka musu wajen yaki da ‘yan ta’addan.



