Kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaro a yankin.
Wata sanarwar bayan taro da kungiyar ta fitar ta hannun mai magana da yawun ta Farfesa Abubakar Jiddere, ta bayyana cewa ta’azzarar matsalar a yankin ta sanya bukatar sanya dokar ta baci don kawo karshen lamarin, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
Kazalika kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta, na kare dukiyoyin da rayukan yan Najeriya.
Dattawan arewacin Najeriya sun bukaci Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan tsaro a yankin
-


