An yi wa shugaban Amurka Joe Biden mai shekaru 82 aikin “kansar” fata, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
Yayin tattaunawa da kafar yada labarai “Fox News”, mai magana da yawun Biden, Kelly Scully, ta tabbatar da cewa an gudanar da aikin kan tsohon shugaban, sai dai bata bayyana nau’in cutar ba.
A baya-bayan nan ne wasu hotuna da bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, suka nuna Biden dauke da “bandeji” da kuma tabo a kan sa.



