DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Fadar shugaban Nijeriya ta fitar da jerin wadanda ba za su biya haraji ba

-

A wata hira da aka yi da Shugaban kwamitin gyaran haraji, Mr Taiwo Oyedele a tashar Channels ranar Talata, 8 ga watan Satumba, ya bayyana cewa sama da kashi 97 na yan Najeriya ba za su biya haraji ba kwata-kwata, Mr Taiwo ya bayyana jerin wadanda biyan sabon harajin ba zai shafe su ba kamar haka.

1. Masu karbar mafi karancin albashi na 70k zuwa kasa.

Google search engine

2. Wadanda kudin shigarsu bai zarce dubu 100 ba a wata.

3. ‘Yan kasuwa masu jarin kasa da Naira Milyan 2.

4. Kamfanoni da a da ake karbar haraji a hannunsu duk da kadararsu ba ta haura milyan 25 ba, yanzu sai kadararsu ta kai Naira Milyan 100 sannan za su biya haraji.

6. Wadanda ke biyan tarin haraje- haraje ma ba a bar su a baya ba, domin daga sabuwar shekarar 2026 za su fara biyan haraji daya tal , kuma mafi karanci.

Ko ta yaya mutum zai gane cewa bai cancanci biyan haraji ba? Mr Oyedele ya ce tuni suka tanadi hatimi a manhajar QR kan shafin yanar gizo na tsarin harajin, inda duk mai bukatar sanin matsayinsa zai je ya dauki hoton hatimin QR din ya zura sunansa da bayanin kudaden shigarsa don sanin ya dace ya biya haraji ko a’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara