Lauyan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Victor Giwa, ya zargi shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio, da amfani da mukaminsa wajen daukar fansa kan ‘yar majalisar.
Giwa ya bayyana haka ne a cikin wata hira da aka yi da shi a shirin siyasar gidan talabijin na Channels a ranar Talata, inda ya bayyana matakin da majalisar dattawan ta dauka a kan Natasha a matsayin bi-ta-da-kulli.
A cewar lauyan, wa’adin hukuncin dakatar da ita na tsawon watanni shida ya cika, amma duk da haka majalisar ta ki amince mata da komawa bakin aiki.
Ya ce wannan hali da ake nuna wa Natasha ya jefa ayar tambaya kan abubuwan da sanatar ta fada a baya, yana mai cewa ya kamata a bari lokaci da tarihi su nuna gaskiya.



