Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama, ya bayyana cewa kasar ta fara karɓar ‘yan ƙasashen Afrika ta Yamma da aka kora daga Amurka, ciki har da ‘yan Najeriya.
Rahoton Reuters ya ce tuni aka saukar da rukunin farko na mutum 14 a Accra, wadanda suka hada da ‘yan Najeriya, wani dan Gambia da kuma wasu daga sauran ƙasashen yankin.
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Donald Trump ke kara kaimi wajen kora ‘yan gudun hijira zuwa wasu ƙasashe matsakaita a matsayin ɓangare na manufofinta kan shige-da-fice.
Rahoton jaridar Punch ya ce, a baya ma Trump ya taba jagorantar korar baki zuwa kasashen Eswatini, Sudan ta Kudu da Rwanda, duk da korafe-korafen kungiyoyin kare hakkin bil’adama game da tsaro.
Sai dai Najeriya ta ƙi karɓar irin wannan tayin daga Amurka, ina a watan Yuli, Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta amince da karɓar ‘yan gudun hijira daga waje ba, saboda dalilan tsaro da tattalin arziki.



