Tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, da dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, sun gana a Abuja a ranar Alhamis.
Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara samun tattaunawa kan yiwuwar jam’iyyun adawa su haɗa kai domin fitar da ɗan takara mai ƙarfi a zaben 2027 domin kalubalantar shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A watan Agusta, wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP sun tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin shawo kan Jonathan ya dawo ya tsaya takarar shugaban ƙasa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Jonathan, wanda ya shugabanci Najeriya daga 2010 zuwa 2015, har yanzu yana daga cikin fitattun ‘yan siyasar ƙasar.
Rahoton jaridar Daily Trust ya ayyana Obi, tsohon gwamnan Anambra na tsawon wa’adi biyu, ya samu karɓuwa sosai bayan zaben 2023, inda ya zo na uku amma ya kayar da Tinubu a jihar Legas, inda shi ne gari da aka fi sanin shugaban ƙasar.



