DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kamfanin mai na Dangote zai fara jigilar fetur kyauta daga ranar Litinin

-

Kamfanin mai na Dangote Refinery zai fara shirin jigilar man fetur kyauta daga ranar Litinin mai zuwa, in ji rahoton jaridar Punch.

Mai magana da yawun rukunin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, ya bayyana a cikin sanarwar cewa shirin zai fara ne daga jihohin Kudu maso Yamma, Abuja, Kwara, Delta, Rivers da Edo.

Google search engine

Ya kara da cewa matatar man ta riga ta rage farashin man fetur zuwa Naira 841 a kowace lita a Lagos da sauran jihohin Kudu maso yamma, yayin da a Abuja, Edo, Kwara, Rivers da Delta za a sayar da shi kan Naira 851 a kowace lita.

A baya dai an shirya fara wannan shiri tun watan Agusta, amma aka samu tsaiko saboda matsalolin sufuri daga kasar China.

Rahotanni sun ce an riga an samu motocin dakon mai sama da 1,000 da za su fara aikin rabon, kuma ana sa ran karin jihohi za su shiga cikin shirin nan gaba kadan yayin da karin manyan motocin ke iso wa Najeriya.

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, kamfanin Dangote ya ce ya kaddamar da motoci 10,000 masu amfani da iskar gas (CNG) domin karfafa jigilar kayayyaki da rage kudin safara a fadin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara