Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce an kusa cimma burin samar da wutar lantarki babu daukewa a fadin kasar.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka a Abuja yayin kaddamar da gine-gine da dakuna a cibiyar horar da ma’aikatan wutar lantarki ta kasa NAPTIN.
Adelabu ya ce wannan ci gaban ya nuna jajircewar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen fifita bukatun al’umma, inda ya ce yanzu haka an samu mafi karfin wutar da aka taba samarwa a tarihin Nijeriya.
A cewarsa nan kusa za a shiga wani zamani da Nijeriya za ta rika samun wutar lantarki ta tsawon awanni 24 ba tare da yankewa ba.
Ya kuma ce Nijeriya na da dukkan abin da ake bukata wajen fara kera na’urorin wutar lantarki kamar mita, transfoma, da batir wanda zai sa ta dogara da kanta.



