DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ƴan majalisar tarayya daga jihar Kebbi sun bukaci jami’an tsaro su kama Malami

-

Wani rikicin siyasa ya kunno kai a jihar Kebbi bayan ‘yan majalisar tarayya daga jihar suka fito fili suna zargin tsohon Ministan Shari’a kuma tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, da yada labarai na karya da suke ganin za su iya jefa jihar da kasa baki daya cikin rudani.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, jagoran ƴan majalisar, Sanata Adamu Aliero, ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta kama tare da gurfanar da Malami a gaban kotu bisa zargin kokarin tayar da tarzoma da tada hargitsi a jihar.

Sanata Aliero ya ce Malami ya shigo da ‘yan daba daga Sokoto da wasu makwabtan jihohi domin su kai hari kan sakatariyar jam’iyyar APC da ke Birnin Kebbi, lamarin da ya janyo artabu tsakanin magoya bayan Malami da ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar.

 
Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon Minista Tanimu Turaki ya zama ɗan takarar shugabancin jam’iyyar PDP na Arewa

Jagororin jam’iyyar PDP na yankin Arewacin Nijeriya sun amince da tsohon Ministan Harkoki. A Musamman, Tanimu Turaki (SAN), a matsayin ɗan takarar da suka amince...

Jam’iyyar ADC a Kaduna ta kori mataimakin shugabanta da wasu ‘ya’yanta 8

Jam'iyyar hadaka ta ADC mai hamayya a Nijeriya reshen Kaduna ta kori mataimakin shugabanta na jihar tare da wasu manyan jami'anta guda takwas, bayan samun...

Mafi Shahara