An fara samun kwanciyar hankali a kasar Nepal bayan da aka nada mace ta farko a matsayin Firaminista na wucin gadi, jim kadan bayan tarzomar zanga-zangar cin hanci da rashawa da ta girgiza kasar.
A ranar Asabar ne babban birnin kasar ya fara komawa daidai, inda aka sassauta dokar hana fita bayan kwanaki da dakarun soja suka mamaye tituna tun ranar Laraba, lokacin da zanga-zangar ta yi sanadin kifar da gwamnati tare da kona majalisar dokokin kasar.
Akalla mutane 51 ne suka rasa rayukansu a wannan tarzoma, mafi muni tun bayan yakin basasa na tsawon shekaru goma da kuma rushe tsarin sarauta a shekarar 2008.
A daren Juma’a, an rantsar da tsohuwar alkalin kotun koli mai shekaru 73, Sushila Karki, a matsayin Firaminista na wucin gadi, domin aikin dawo da doka da oda da kuma sauraron bukatun masu zanga-zangar da ke neman kawar da cin hanci da rashawa.
Bayan haka, an rusa majalisar dokoki, aka kuma ayyana ranar 5 ga Maris, 2026 a matsayin ranar zabe, tare da soma kokarin gina sabuwar gwamnati.


