Dakarun rundunar sojin Najeriya ta 12 Brigade, karkashin Operation Accord III, tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro, sun yi nasarar halaka wani kwamandan ‘yan bindiga mai suna Babangida Kachala, wanda shi ne mataimakin shugaban dabar da Kachala Shuaibu ke jagoranta a dajin Masalaci Boka da Ofere, Jihar Kogi.
Wannan nasarar ta zo ne mako guda kacal bayan da sojoji suka yi nasarar kashe wani babban kwamandan dabar, Kachalla Balla, tare da wasu ƴan bindiga biyar.
Haka kuma, dakarun tare da tallafin jiragen sama sun gudanar da wasu hare-haren share fagen da ya kai ga ceto fursunonin da aka sace.
Mai magana da yawun rundunar, Lieutenant Hassan Abdullahi, wanda shi ne mukaddashin daraktan hulɗa da jama’a na 12 Brigade, ya tabbatar da wannan nasara a cikin wata sanarwa da aka fitar daga Lokoja a ranar Asabar.
