Bayanai daga hukumar da ke kula da shige da fice da ‘yan gudun hijira ta kasar Canada sun nuna cewa akalla bukatar’ yan Najeriya 1,596 na neman mafaka ne aka yi watsi da su a shekarar 2025.
Jaridar punch ta tattaro cewa zuwa ranar 21 ga watan Agusta, kasar ta samu jimillar bukatar neman mafaka daga ‘yan Najeriya 3,548 inda aka karbi 2,292 daga ciki.
Wani bincike da cibiyar Maple Crest Law ta gudanar a Canada, ya nuna cewa matsalolin tsaro, da taɓarɓarewar tattalin arziki a Najeriya na daga cikin dalilan da suka sa neman mafaka a Canada da sauran kasashe ya yawaita.



