Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin naɗa wani tsohon alkalin kotun daukaka ƙara a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC.
Da yake magana a wani shiri da gidan talabijin na Arise, Galadima ya bayyana cewa wannan alkalin da ake yada jita-jita a kansa, zai iya zama barazana ga sahihancin sakamakon zaɓukan 2027, inda ya yi gargadin cewa hakan na iya jefa Najeriya cikin rikici.
Galadima ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da rashin mutunta dokar ƙasa, inda ya ce tuni an riga an lalata sahihancin INEC domin fifita jam’iyyar APC.
Ya yi nuni da cewa an taɓa naɗa wani da ya rike muƙamin sakatare a jam’iyyar APC kuma ya yi aiki a kotu, daga bisani aka ba shi shugabancin INEC.



