Bayanan da jaridar Punch ta tattaro sun ce malamin jami’a a Nijeriya da ya kai matakin farfesa na samun matsakaicin albashi na dala 366 (kimanin Naira 500,000) a wata, wanda ya yi kasa kwarai da na takwarorinsu a wasu kasashen nahiyar.
Bayanan da suka shafi albashin farfesoshi a jami’o’in gwamnati na nahiyar Afrika sun bayyana cewa yayin da farfesa a Nijeriya ke samun kusan dala 4,400 a shekara, farfesa a Afirka ta Kudu na samun dala 57,471 a shekara, wanda ya ninka fiye da sau 13.
Uganda na biye da dala 50,595 a shekara, sai Kenya da dala 48,000 a shekara, yayin da ƙasashen da tattalin arzikinsu bai kai na Nijeriya ba, irin su Eswatini (dala 41,389), Lesotho (dala 32,455), da Gabon (dala 29,907), suke biyan albashin farfesoshi a shekara.