Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta maka dan gwagwarmaya Omoyole Sowore, kamfanin Meta da kuma manhajar X kotu, sakamakon kalaman sukar gwamnatin Tinubu da Sowore ya wallafa.
Hukumar ta shigar da karar ne a gaban wata kotun tarayya da ke Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wannan ya biyo bayan da hukumar DSS din ta bukaci a dakatar da shafin na Sowore a baya, tare da ba shi wa’adin goge wallafar da ya yi.
Sai dai a martaninsa, Sowore ya sha alwashin halartar kotun kan karar da hukumar ta shigar.



