DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Manoma a Nijeriya sun koka kan shirin karya farashin kayan abinci

-

Manoma da masu sarrafa shinkafa a Najeriya sun soki manufofin gwamnatin tarayya bayan da alkaluma suka nuna cewa yawan kudaden shigo da kayayyakin gona ya kai Naira tiriliyan 2.22 cikin watanni shidan farko na shekarar 2025.

Rahoton jaridar Punch ya ce, a kwanakin baya ma, Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarni ga kwamitin majalisar zartarwa na tarayya da ya tabbatar da saukar farashin abinci a duk fadin kasar.

Google search engine

Karamin ministan noma da tsaron abinci, Sabi Abdullahi, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin taron horas da manema labarai na majalisar dattawa.

Sai dai wannan umarni ya gamu da suka daga manoma da masu sarrafa shinkafa, wadanda suka ce tsarin cinikayyar kayan amfanin gona zai fada cikin rudani, maimakon daidaita shi.

Ya kara da cewa mafi dacewa shi ne gwamnati ta kira manyan masu ruwa da tsaki a harkar noma da sufuri, a tattauna da su tare da samar da tallafi kafin bayar da irin wannan umarni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara