Mamallakin matatar mai ta Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa shekaru akalla 50 da aka shafe a Najeriya ana fama da dogayen layuka a gidajen mai ya kawo karshe, tun bayan da matatar sa ta fara aikin tace fetur a shekarar da ta gabata.
Dangote ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron cika shekara guda da fara aikin matatar, inda ya ce tun daga shekarar 1975 ‘yan Najeriya ke fama da dogayen layukan.
Sai dai yace daga ranar 15 ga watan Satumban 2024 wannan matsala ta kau, biyo bayan fara aiki gadan-gadan, kamar yadda Channels TV ya wallafa.
Kazalika ya jaddada kudirin matatar man Dangote na ganin ta ciyar da Najeriya da ma nahiyar Afirka gaba.



