Rundunar ’yan sandan jihar Neja ta sanar da kama mutane hudu bisa zargin sata da kuma karɓar kayan sata, bayan da aka sace kifaye da kimar kudinsu ta kai Naira 750,000 daga wani gidan gona a Lapai-Gwari, karamar hukumar Chanchanga.
Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa a ranar 8 ga Satumba, 2025, wasu mutane biyu, Hussaini Garba da Umar Danfulani, dukkansu daga Lapai-Gwari sun hada baki, tare da sace kifin a lokuta daban-daban.
Ya ce daga bisani an kama Garba, kuma yayin bincike ya amsa laifin, inda ya bayyana sunayen mutanen da ya ba su kifin da aka sace.
Rundunar ’yan sandan ta tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike tare da farautar sauran masu laifi, tare da ba da tabbacin cewa za a gurfanar da duk wanda aka kama da aikata irin wadannan laifuka domin kare al’umma a Jihar kamar yadda Jaridar Punch ta Ambato.



