Hukumomi a Saudiyya sun saki Maryam Abdullahi Hussaini, ‘yar asalin Nijeriya daga jihar Kano, wadda aka tsare a Makkah bisa zargin ta da jaka mai dauke da miyagun kwayoyi.
Kazalika, an kuma saki wasu ‘yan Nijeriya biyu Abdullahi Bahijja Aminu da Abdulhamid Saddiq da su ma suka fuskanci irin wannan tuhuma.
Maryam, ta samu ‘yancin ne bayan kwashe sama da mako biyar a tsare, sakamakon shiga tsakani da gwamnatin Nijeriya da kuma tabbatarwar da hukumar NDLEA ta yi cewa ba ta da laifi.
Jaridar Premium times ta rawaito cewa mijin matar Abdullahi Baffa, ya tabbatar da sakin nata, inda ya bayyana farin cikinsa tare da gode wa Allah da dukkan masu hannu a lamarin.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya NDLEA ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya gano cewa matasa masu safarar miyagun ƙwayoyi a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano ne ke shirya makirci, ta hanyar saka sunayensu jakunkuna da ba na fasinjojin ba.
An kuma tabbatar da cafke shugabansu Mohammed Ali Abubakar, da wasu daga cikin mabiyansa, wadanda ke da hannu wajen sakawa fasinjojin da ba su da laifi cikin wannan tarkon.



