Babban bankin Najeriya CBN, ya gargadi ’yan ƙasar da su guji liki da takardun Naira, lalata wa ko yin jabun kuɗin Nairar, yana mai bayyana ta a matsayin takarda mai daraja.
Mataimakiyar daraktan hulɗa da jama’a na bankin CBN, Hajiya Hakama Sidi Ali, wacce ta wakilci gwamnan bankin, Mista Olayemi Cardoso, ta bayyana haka a bikin CBN Fair da aka gudanar a Kaduna.
Rahoton jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa CBN Fair dandalin ne da bankin ke amfani da shi wajen tattaunawa da jama’a kan manufofinsa domin samar da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
Ta kuma shawarci ’yan Najeriya da su rika neman bayanai daga sahihan hanyoyin samun bayanai daga bankin, domin gujewa fadawa cikin yaudara da labaran karya.



