Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na kasar China, Xi Jinping, sun yi magana ta waya a ranar Juma’a, inda suka mayar da hankali kan makomar manhajar TikTok da kuma alakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Tattaunawar ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatocin kasashen biyu ke nazartar matakan da ka iya sauya yanayin dangantakar tattalin arziki a bangaren tsakanin Washington da Beijing.