Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Nijeriya NCAA ta zargi kamfanin jiragen saman Qatar Airways da wulakanta dokokin ƙasar, musamman ta fuskar walwalar fasinjoji, tare da yin gargaɗi cewa za ta ɗauki matakan ladabtarwa masu tsauri kan kamfanin.
Jami’in hulɗa da jama’a hukumar ta NCAA, Michael Achimugu, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a.
Achimugu ya bayyana cewa wani fasinja ɗan Nijeriya da ya tashi daga Lagos zuwa Amurka tare da matarsa, inda wani jami’in jirgin na Qatar Airways ya zarge shi da yin halayya mara kyau.
A cewarsa, ba a kawo wannan zargi a Lagos ba, sai da suka isa birnin Doha na Qatar, inda aka kama fasinjan, aka tsare shi na tsawon awanni 18, sannan aka ci shi tara mai yawa.
A cewarsa hukumomi a Doha sun tilasta wa fasinjan sa hannu a kan wata takarda da aka rubuta da harshen Larabci kawai, saboda tsananin buƙatar samun a sakeshi, ya sa hannu ba tare da fahimtar abin da ke cikin takardar ba,kuma duk da haka aka tilasta masa sayen sabon tikiti.
Bayan faruwar lamarin, NCAA ta gayyaci Qatar Airways domin tattaunawa, amma Achimugu ya ce manajan kamfanin na kasar ya ƙi zuwa ya aika da kananan ma’aikata.



