Rahoton gidan talabijin na Channels ya Ambato ministan cikin gida na Nijeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa Hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) yanzu tana iya samar da fasfo tsakanin 4,000 zuwa 5,000 cikin awa biyar karo na farko cikin shekaru 62.
Tunji-Ojo ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, bayan ya duba sabuwar cibiyar samar da fasfo da aka gina a hedikwatar hukumar shige da fice ta Nijeriya da ke Abuja.
A cewar sa, sabuwar fasahar ta baiwa hukumar damar yin fiye da fasfo 1,000 a cikin awa guda, alhali a da hukumar tana iya yin tsakanin fasfo 250 zuwa 300, ne a rana kacal.



