Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta tabbatar da cewa mutum uku sun rasa rayukansu, yayin da gidaje sama da 1,415 suka shiga halin tsaka mai wuya sakamakon ambaliyar ruwa da ta biyo bayan ruwan sama a Jihar Adamawa.
Lamarin ya auku ne a ranar Talata a ƙananan hukumomin Yola ta Arewa da Yola ta Kudu.
Rahoton hukumar ya nuna cewa mutane sama da 40 sun jikkata, yayin da gonaki da muhimman gine-gine suka cika da ruwa, lamarin da ya tilasta wa daruruwan iyalai kauracewa gidajensu.
Hukumar ta ce bincike gaggawa da ofishin ta na Yola ya gudanar tare da haɗin gwiwar hukumar ADSEMA da sauran masu ruwa da tsaki ya gano cewa ƙauyuka 13 ne abin ya shafa.



