Ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike, ya amince da dukkan bukatun likitoci masu neman kwarewa da suka shiga yajin aiki tun ranar 15 ga Satumba, saboda batun albashi da alawus-alawus din su.
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin kaddamar da aikin gina hanyar Northern Parkway daga Ring Road II zuwa Ring III a kan titin Shehu Yar’Adua, a birnin Abuja.
Haka kuma, ya umurci mukaddashin Shugaban ma’aikatan FCT tare da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin gudanarwa, Samuel Atang, da su aiwatar da umarnin yadda ya kamata.
Rahoton kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya tuna cewa likitocin sun shiga yajin aiki bayan doguwar tattaunawa da hukumar FCTA ba tare da samun mafita ba.



