Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya ce bai kamata a sake zabar duk shugaban da ya gaza sauke nauyin da ke kansa ba, muddin ana gudanar da sahihin zabe.
Yayin gudanar da taron gidauniyar Goodluck karo na 25 a birnin Accra na kasar Ghana, Goodluck ya bayyana magudin zabe a matsayin mafi girman barazana ga dimukuradiyyar Afirka.
Daily Trust ta ruwaito tsohon shugaban na cewa akwai bukatar dukkanin masu ruwa da tsaki su hada hannu wajen kawo sauyi a dimukuradiyyar nahiyar, domin ceto ta daga rushewa.



