Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma bakin aiki a ranar Talata, 23 ga Satumba, 2025, bayan Majalisar Dattawa ta buɗe ofishinta da aka rufe tun lokacin da aka dakatar da ita.
Ofishin nata da ke Suite 2.05 a ginin majalisar an buɗe shi ne a safiyar Talata, abin da ya bai wa Sanatar damar komawa cikin gaggawa don ci gaba da aikinta.
Tun a baya dai an dakatar da Sanatar na tsawon watanni shida, abin da ya janyo cece kuce a siyasar jihar Kogi da ma a tsakanin ‘yan Nijeriya da dama.



