DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tattalin arzikin Nijeriya ya bunkasa da kaso 4.23% cikin 2025, in ji hukumar NBS

-

Hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS ta ce tattalin arzikin kasar ya ƙaru da kashi 4.23 cikin ɗari a ma’aunin tattalin arziki na GDP a zango na biyu na shekarar 2025 idan aka kwatanta da shekarar 2024.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin rahoton GDP na Najeriya na zango na biyu na shekarar 2025 da ta fitar a Abuja a ranar Litinin. Rahoton ya nuna cewa wannan ci gaban ya fi kashi 3.48 da aka samu a zango na biyu na 2024, haka kuma ya fi kashi 3.13 da aka samu a zangon farko na 2025.

Google search engine

A cewar rahoton, bangaren noma ya samu ci gaban kashi 2.82 idan aka kwatanta da kashi 2.60 da aka samu a zango na biyu na 2024. Bangaren masana’antu ya samu ci gaban kashi 7.45, wanda ya ninka kashi 3.72 da aka samu a zango na biyu na 2024. Bangaren ayyuka kuma ya samu kashi 3.94 idan aka kwatanta da 3.83 na zango na biyu na 2024.

Rahoton ya ce a cikin zango na biyu na 2025, darajar GDP ta kai Naira tiriliyan 100.73, idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 84.48 da aka samu a zango na biyu na 2024, wanda ya nuna ci gaban shekara zuwa shekara da kashi 19.23.

Haka kuma, bangaren mai ya samu ƙarin kashi 6.01 a zango na biyu na 2025 idan aka kwatanta da zangon farko na 2025. Bangaren ya bayar da gudummawar kashi 4.05 cikin ɗari ga GDP, idan aka kwatanta da kashi 3.51 na zango na biyu na 2024 da kuma 3.97 na zangon farko na 2025.

Rahoton ya kuma nuna cewa matsakaicin adadin fitar da man fetur ya kai ganga miliyan 1.68 a kullum a zango na biyu na 2025, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.41 da aka samu a zango na biyu na 2024, da kuma ganga miliyan 1.62 a zangon farko na 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara