Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya kaddamar da sabon shirin rigakafi a Nijeriya domin yakar sabon nau’in cutar kyanda da za a yi shi tare da rigakafin cutar shan inna polio a dukkan jihohi 36 na kasar.
Shugaban ofishin asusun UNICEF na Kano, Rahama Farah, ya bayyana cewa za a gudanar da shirin a matakai biyu, daga Litinin, 6 ga Oktoba, 2025, zuwa Juma’a, 13 ga Fabrairu, 2026.
Farah ya yi wannan bayani ne a Katsina, yayin taron tattaunawa da manema labarai wanda UNICEF hade da Gwamnatin Jihar Katsina suka shirya kan shirin rigakafin.
Ya ce, an samar wa jihar Katsina da kaso 3,698,500 na maganin rigakafin shan inna (Novel Oral Polio Vaccines – nOPV2), inda ake sa ran yi wa yara miliyan 2.3 da ba su kai shekaru biyar ba, waɗanda za a yi musu rigakafin ta tsarin Directly Observed Oral Polio Vaccination (DOOPV).
Haka kuma, a cikin wannan yakin, za a yi wa yara miliyan 4.8 daga watanni 9 zuwa shekaru 14 rigakafin sabon nau’in kyanda da ake kira da “rubella”.



