Uwargidan shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta yi watsi da zarge-zargen cewa Naira biliyan 20 da ‘yan Najeriya suka tara cikin asusu a bikin cikar ta shekaru 65 na da alaka da shirin shugaba Tinubu na zaben 2027.
Jaridar Punch ta ruwaito mai dakin shugaban na cewa cikin kasa da mako guda da sanarwar da ta yi, an tara Naira biliyan 20 da miliyan 400 wanda ta ce za a yi amfani da shi ne wajen karasa aikin ginin É—akin karatu na kasa.
Ta kara da cewa wannan ba shi ne karo na farko da ta ke bude asusu don yin wani aikin ci-gaban Najeriya ba.




