DCL Hausa Radio
Kaitsaye

FBI ta nemi taimakon jama’a don kama ɗan Najeriya da ya tsere tun 2001

-

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta sanya kyautar dala 10,000 ga duk wanda ya bayar da sahihin bayani da zai kai ga kama wani ɗan Najeriya mai suna Olumide Adebiyi Adediran, da ake nema bisa tuhumar aikata laifukan zamba a kasar.

A cewar sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon hukumar ranar Laraba, Adediran, mai shekara 56, yana fuskantar tuhumar zamba ta banki, zambar takardun shaidar katin karya (ID fraud), da kuma zambar katin cirar kudi (credit card fraud) a jihar Illinois tun daga shekarar 2001.

Google search engine

FBI ta bayyana cewa Adediran ya tsere daga Central District of Illinois a ƙarshen watan Disambar 2001, kwanaki kafin fara shari’arsa.

Gidan jaridar Punch ya ruwaito cewa, a ranar 2 ga Janairu, 2002, kotun tarayya a Illinois ta bayar da takardar izinin kama shi (arrest warrant) bayan ya karya sharuddan belinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tinubu ya gargadi Alkalan Nijeriya da kada su karkata ga cin hanci ko rashin adalci

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga alkalai da sauran ma’aikatan shari’a a Najeriya da su ci gaba da zama masu gaskiya, adalci,...

PDP ta musanta zargin kirƙirar sa hannun Sakataren ta na kasa

Kwamitin zartaswa na Ƙasa na jam’iyyar PDP ya musanta zargin ƙirƙirar sa hannu da Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya yi. Mai magana da...

Mafi Shahara