DCL Hausa Radio
Kaitsaye

FBI ta nemi taimakon jama’a don kama ɗan Najeriya da ya tsere tun 2001

-

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta sanya kyautar dala 10,000 ga duk wanda ya bayar da sahihin bayani da zai kai ga kama wani ɗan Najeriya mai suna Olumide Adebiyi Adediran, da ake nema bisa tuhumar aikata laifukan zamba a kasar.

A cewar sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon hukumar ranar Laraba, Adediran, mai shekara 56, yana fuskantar tuhumar zamba ta banki, zambar takardun shaidar katin karya (ID fraud), da kuma zambar katin cirar kudi (credit card fraud) a jihar Illinois tun daga shekarar 2001.

Google search engine

FBI ta bayyana cewa Adediran ya tsere daga Central District of Illinois a ƙarshen watan Disambar 2001, kwanaki kafin fara shari’arsa.

Gidan jaridar Punch ya ruwaito cewa, a ranar 2 ga Janairu, 2002, kotun tarayya a Illinois ta bayar da takardar izinin kama shi (arrest warrant) bayan ya karya sharuddan belinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tinubu ya aika da sunan Dr. Bernard Mohammed ga majalisa don nada shi minista

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunan Dr. Bernard Mohammed Doro daga jihar Filato ga majalisar dattawa don nada shi minista a gwamnatinsa. Bayanin...

Osinbajo ya isa Cote d’Ivoire don jagorantar sa ido kan zaben kasar

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya isa Cote d'Ivoire domin Jan ragamar masu sanya ido kan zaben kasar da zai gudana a ranar...

Mafi Shahara