DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Nijeriya ta fifita tara kudaden shiga kan rayukan talakawa – Atiku Abubakar

-

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya nuna takaici cewa ana rasa rayuka a ƙasar yayin da gwamnati ke ta bikin cika burin tara kuɗin shiga.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, Atiku ya yi Allah wadai da harin ’yan ta’adda a kauyen Wagga Mongono da ke karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa, wanda ya ce ya sake fito da cewa matsalar tsaro ba ta gushe ba a Najeriya.

Google search engine

Rahotan da gidan talabijin na Channels ya tattaro sun bayyana cewa harin da aka kai ranar Talata ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum huɗu, wasu da dama sun jikkata, sannan aka ƙone gidaje, shaguna da wata coci, abin da ya tilasta mazauna yankin da dama tserewa zuwa dazuzzuka.

Atiku, wanda ya fito daga jihar Adamawa, ya bayyana cewa wannan lamari ya taba shi kai tsaye, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara