Wani bincike da jaridar Premium Times ta gudanar ya nuna cewa ba Kano ce ta fi kowace jiha a Najeriya cin jarrabawar NECO ta shekarar 2025 ba.
Jaridar ta ruwaito cewa Kano ta zama kan gaba ne a yawan wadanda suka zauna jarrabawar, inda sama da kaso 10 suka fito daga jihar.
Haka kuma ta ce kaso 5 na wadanda suka zana jarrabawar ne suka samu maki biyar da ake bukata, wanda ya hada da darussan Turanci da Lissafi.
Kazalika ta ce Kano ba ta zarta jihohin Oyo da Legas ba, kamar yadda gwamnatin Kano ta yi ikirari.