Kungiyar nan da ke sa ido kaneyadda aikin hajji ke gudana a Nijeriya Independent Hajj Reporters ta ce Naira milyan 6.8 ya kamata a biya kudin aikin hajjin 2026 mai zuwa.
Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON a ranar Asabar ta sanar da kudin hajjin 2026 na ‘yan Najeriya da ke shirin zuwa aikin hajji, inda ta ce maniyyata daga Kudancin Najeriya za su biya N8,561,013.67, yayin da na Arewacin kasar za su biya N8,244,813.67, sai kuma daga arewa maso gabas (Borno, Yobe da Adamawa) za su biya N8,118,333.67 don aikin hajjin 2026.
NAHCON ta ce an cimma wannan kudin ne bayan tattaunawa da hukumomin alhazai na Jihohin kasar. Bambance-bambancen da ake samu, kamar yadda aka saba, daga kudin jirgi ne na zuwa da dawowa daga Saudiyya.
Sai dai a cikin kididdigar da Ibrahim Muhd babban jami’in kungiyar IHR ya yi, kungiyar ta yi wasu tambayoyin cewa, shin NAHCON ta kammala lissafin kuɗin masaukin maniyyata a Makka da Madina? Shin an kammala kudin abinci a Makka da Madina? Shin kamfanonin jiragen sama sun amince da ci gaba da amfani da kudin tikitin bara, ko kuwa akwai karin kuɗi?
Amma idan aka kwatanta da hajjin 2024, kudin 2026 ya ƙaru da kusan N3.6m. Hajjin 2026 ya ƙara wasu abubuwan amfani idan aka kwatanta da 2025, amma idan aka kwatanta da 2024, ya zama nauyi.
A lokacin hajjin 2024, maniyyata daga Kudu sun biya N4,899,000, daga Arewa N4,699,000, sai daga Yola da Maiduguri N4,679,000.
Wannan bai haɗa da tallafin da gwamnatin tarayya ta bayar ba na Naira biliyan 90, inda aka ce kowanne maniyyaci ya amfana da kusan N1m.
A tsarin kudin hajjin 2025 akwai ayyuka 25. Ayyuka 11 daga ciki aka kidaya ne a kan farashin N1,600/$1, duk da cewa lokacin biyan hajjin 2025 dalar Amurka ta tsaya a N1,520/$1. Wato ciniki bai kammala ba.
Yanzu, wane kudin musayar kudi aka yi amfani da shi wajen lissafin kudin hajjin 2026? Kuma nawa ne za a bayar a matsayin BTA ga maniyyata?
A hajjin 2025, kowanne maniyyaci ya samu $500, inda ya biya N800,000 don BTA. Yanzu nawa ne a daloli da kuma naira?
A yau, kudin musayar ya tsaya a N1,492/$1. Wannan ya nuna cewa farashin dalar 2026 ya fi na 2025 sauƙi.
Jimillar kuɗin dalar Amurka a hajjin 2025 ita ce $4,622. Idan aka juya da farashin yanzu (N1,492/$1), zai bada N6,872,266.92.
Ƙananan kuɗaɗen cikin gida a hajjin 2025 sun kasance N36,000, waɗanda suka haɗa da kuɗin gudanarwa na NAHCON, harajin ci gaba, kayayyaki (uniforms), katin ƙyellow fever, kuɗin gudanarwa na jihohi da takardun rajista.
Idan waɗannan basu canza ba, kuma babu karin kuɗaɗen da suka shafi ayyukan da za a yi a Saudiyya, to kudin hajjin 2026 ya kamata ya kasance N6,857,398.32 tare da ƙarin kuɗin cikin gida N36,000, wanda gaba ɗaya zai zama N6,893,398.
Sai dai idan an sake amfani da wata matsakaiciyar farashin dalar gaba kamar yadda aka yi bara.
Ibhmrahum Muhammad ya ce wannan hasashe nashi ya ta’allaka ne a kan gogewa cewa dukkan ayyukan hajji ana lissafinsu cikin tsarin kudin hajji, har ma da BTA daidai da nairarsa – a kalla haka aka saba lokacin da Uba Mana yake shugaban yada labarai na NAHCON.
A bara, maniyyata daga Arewa sun biya N8,457,685.59, daga Kudu N8,784,085.59, sai kuma daga yankin Borno N8,327,125.59.
Saboda haka, akwai ragin kusan N218,000 zuwa N220,000 a kudin 2026 idan aka kwatanta da na 2025. Wannan abin yabawa ne ga hukumar.