Tsohon Ministan yada labaran Nijeriya Farfesa Jerry Gana, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan zai tsaya takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Jerry Gana ya kuma nuna kwarin guiwa cewa Jonathan zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin dawo da mulki bayan shafe shekaru goma da barinsa.
A cewar Gana, ‘yan Najeriya sun dandana mulkin shugabanni biyu bayan Jonathan, kuma a halin yanzu suna mararin ya sake dawowa.