Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar ya yi tsokaci game da jawabin murnar ‘yancin kai da Shugaba Tinubu ya gabatar, inda ya ce duk kanzon kurege ne.
A safiyar Laraba shugaba Tinubu ya yi jawabi wanda a ciki yake nuna yadda ya sauya akalar ayyuka tare da dasa tubali mai kwari ba na toka ba, tare da bayyana nasarori a bangarorin ilimi, kiwon lafiya, tattalin arziki da tsaro.
Sai dai, Atiku ya yi masa raddi ta hannun mai taimaka masa wajen hulda da jama’a Phrank Shuaibu inda ya ce ba giringirin ba, ta yi mai, matukar mutane na kwana da yunwa, aikin kawai ne.
Haka kuma, ya ce shugaba Tinubu na takama da karuwar makarantu daga shekarar 1960 zuwa yanzu amma kuma a kasa yara ke zama suna rubutu a yashi a makarantu da dama, yayin da albashin malaman ba zai iya ci da su ba.



