Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana cire tallafin man fetur da cewa ba abu ne mai sauki ba, amma mataki ne da ya zama wajibi domin ceto tattalin arzikin kasar ta yadda kowa zai amfana.
Shugaba Tinubu ya fadi haka ne a jawabin da ya yi wa ‘yan kasa a ranar Laraba domin murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
Haka kuma, ya bayyana yadda ya gaji tattalin arzikin da ya kusan rushewa wanda hakan ya tilasta daukar matakai masu tsauri.
Tinubu ya kara da cewa, an yi amfani da kudaden da aka yi rara sakamakon cire tallafin man fetur a bangarorin ilimi, tsaro, lafiya da noma domin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.



