Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti Uduaghan ta bayyana damuwa da cewa, Nijeriya ba za ta samu sauyi na gaske ba har sai an samu nagartaccen shugabanci.
Natasha ta fadi haka ne a sakonta na murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
A cikin jawabin nata, Uduaghan ta siffanta Nijeriya a matsayin kasa mai fama da matsalolin tsaro, matsin tattalin arziki, rashin daidaito amma duk da haka ta jajirce wajen kirkire-kirkire na basira.
A cewarta, Nijeriyar da magabata suka hango ba kasa ce wadda ta rabu sakamakon kabilanci ko addini ko siyasa ba sai dai wacce adalci, daidaito da arziki ya hada kan al’ummarta.



