Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa soke faretin bikin cikar kasar shekara 65 da samun ’yanci ya ba shi damar yin barci tare da samun natsuwa a ranar bikin.
Tun da fari gwamnatin tarayya ta sanar da soke faretin da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba, 1 ga Oktoba 2025, domin bikin ranar ’yancin kai.
Wannan sanarwar ta fito ne daga ofishin Sakataren gwamnatin tarayya, inda aka bayyana cewa daukar matakin ba zai rage muhimmancin wannan rana mai tarihi ba.
A jawabin da ya yi ranar Laraba a wajen kaddamar da cibiyar raya al’adu ta Wole Soyinka a Legas, Tinubu ya ce soke faretin ya ba shi damar samun hutu, yin barci cikin natsuwa tare da samun damar halartar gagarumin bikin.



