Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan bukata ta taso, zai iya hakura da burinsa na neman shugabancin kasa a zaben 2027, domin bai wa wani matashi dama.
Atiku, wanda ke cikin manyan jagororin jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da kafar yada labarai ta BBC Hausa ranar Laraba.
Ya ce idan wani matashi ya kayar da shi a zaben fidda gwani, zai mika wuya ya kuma goya masa baya da karfinsa da shawarwari.
Ya bayyana cewa babban burinsa a yanzu shi ne ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar ADC, wacce a cewarsa ke ba da fifiko ga matasa da mata domin sanyasu a gaba.



