Tsohon ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami ya zargi ‘yan dabar siyasa da kai wa tawagarsa hari a lokacin da ya je Argungu daurin aure a ranar Juma’a.
A cikin wata sanarwa da Mohammed Bello Doka ya fitar, ta ce Malami ya je Sabon Garin Kanta Argungu ne domin halartar daurin aure ne aka kai masa farmakin.
Sanarwar ta kuma ce lamarin ya faru ne jim kadan bayan kammala daurin auren, inda shi da tawagarsa suka tsaya wani masallaci domin su yi sallah, kwatsam sai ga wasu gungun matasa daga sassa daban-daban rike da muggan makamai suna furta kalaman da ke iya tayar da tunzuri.