Wasu majiyoyi sun tabbatar wa da jaridar Punch cewa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, na duba yiwuwar shiga jam’iyyar hadaka ta ADC.
Majiyoyin daga ADC sun ce tabbas Goodluck na duba yiwuwar hakan, sai dai ba su da hurumin yin magana, dalili kenan da ya sanya suka bukaci a sakaye sunayensu.
Wannan ya zo a daidai lokacin da jam’iyyar ta ADC ke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zaben 2027 da karfinta, a wani yunkuri na kawo karshen mulkin APC a siyasance.