Tsohon gwamnan jihar Edo kuma dan majalisar dattawa Sanata Adams Oshiomole ya shawarci tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da ya kare kimarsa ta hanyar kin bin kiraye-kirayen ya tsaya takara a zaben 2027.
Yayin hira da gidan talabijin na Channels cikin shirin siyasa, Oshiomole ya ce makiyin Jonathan ne kawai zai ingiza shi ya tsaya takarar shugabancin kasar.
Ya kara da cewa ko da ya tsaya ba zai yi nasara ba, saboda yana da tabbacin cewa jam’iyyar APC za ta kayar da shi.