Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL Bashir Ojulari, ya ce suna shirin kara adadin ganagar man da ake hakowa zuwa miliyan 1 da dubu dari 8 kafin karshen shekarar 2025.
Ojulari ya bayyana haka ne a tattaunawa da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Tinubu a fadarsa da ke Abuja, inda ya bayyana masa halin da kamfanin ke ciki tare da ayyukan da suka sanya a gaba.
Ya ce sun samu gagarumar nasara wajen samar da mai da iskar gas inda ake samar da ganga miliyan 1.68 a rana a cikin watan Satumban da ya gabata.
Hakazalika, ya ce shugaba Tinubu ya umurce su da su kara adadin zuwa ganga miliyan 3 kafin nan da shekarar 2030.



